• Leadership Hausa
Sunday, June 4, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru Sakamakon Zanga-Zangar Da Ta Barke A Isra’ila

by Ammar Muhammad
2 months ago
in Labarai
0
Muhimman Abubuwan Da Suka Faru Sakamakon Zanga-Zangar Da Ta Barke A Isra’ila
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

An shiga mako na 12 ke nan ana tafka zanga-zanga a kasar Isra’ila. Dubban daruruwa mutane ne ke sake fitowa a kowacce rana suna shiga sahun masu zanga-zangar tare da yin Allah-wadai da gwamnantin Benjamin Netanyahu bisa bullo da dokar kwace ikon bangaren shari’a.

Zanga-zangar wacce tunda farko ta soma da mutane kalilan ta fara ci kamar wutar daji a kasar ganin yadda ta soma karbuwa a wurin wasu jami’an gwamnati da ma’aikata da suke adawa da sabuwar dokar da Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya bullo da shi.

Rahotanni daga kafafen watsa labaran kasar sun tabbatarda cewa ya zuwa yanzu muhimman abubuwa sun faru daga farkon zanga-zangar zuwa hada wannan rahoton.

Abubuwan da suka faru sune kamar haka;

  1. An rufe kafatanin gidajen abinci, cibiyoyin lafiya, ofisoshin gwamnati, ma’aikatar kudi, Babban Bankin kasar Isra’ila, tasoshin zirga-zirga da na ababen hawa, an kulle jami’o’in kasar, wuraren tarihi, shagunan sayayya, da sauran muhimman wurare.
  2.  Dukkanin ma’aikatan wadannan wurare sun tafi yajin aiki tare da shiga cikin zanga-zangar da take ci gaba da kazancewa a Haramtacciyar kasar ta Isra’ila.
  3.  An rufe ofishin Jakadancin Isra’ila da ke birnin Washington da wasu wuraren hulda da Isra’ila da ke Amurka domin nuna goyon baya ga masu zanga-zangar.
  4. Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana yi wa masu zanga-zangar barazanar shekar da jinanensu ta hanyar shirin jami’an ko ta kwana. Inda jami’an ke antaya wa masu zanga-zangar ruwan zafi da barkonon tsohuwa tare da dukan masu zanga-zangar.
  5.  Masu zanga-zangar na kara yawa a kowacce rana inda bayanai ke tabbatar da cewa dubban daruruwa ne a yanzu ke kira da gwamnatin Netanyahu da ta janye kudurin dokarta, idan ba haka ba za su ci gaba da zanga-zangar har sai mama ta gani.
  6.  Masu zanga-zangar na zuwa muhimman wurare a Isra’ila suna shigar da kokensu. A inda suka je har kotun kolin kasar. Zanga-zangar har wala yau ta karade har cikin babbar kasar na TelAbib.
  7. Kungiyar kwadago mafi girma a kasar ta tafi yajin aiki na kafatanin ma’aikata inda ta bukace su da su tafi yajin aiki da kuma shiga cikin masu zanga-zangar.
  8. Fiye da shugabannin garuruwa 24 ne suka tafi yajin aikin cin abinci domin tursasawa gwamnatin Netanyahu.
  9. Asaf Zamir, wanda shi ne Babban Jami’in lura da ofishin Jakadancin Isra’ila na birnin New York ya ajiye aikinsa a wani mataki na goyon bayan masu zanga-zanga tare da Allah-wadai da gwamnatin Netanyahu bisa korar ministan tsaron kasar.
  10. Ministan kudin Isra’ila cikin firgici ya ce dole ne Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya saurari koken masu zanga-zangar. Inda ya goyi bayan masu zanga-zangar tare da yin kira da masu zanga-zangar su yi tururuwa a birnin Jerusalem. Wannan furuci na sa ya sanya Firaministan kasar Isra’ila, ya sauke ministan tsaron.
  11.  Shugaba Biden na kasar Amurka ya ce dole ne hukumomi a Isra’ila su yi takatsantsan tare da yin sulhu da masu zanga-zangar.
  12. Sai dai sakamakon yadda zanga-zangar kullum take kara tumbatsa a kasar, tare da barbazuwa a sassan kasar daban-daban da kuma matsin lamba da Firaminista Netanyahu ke fuskanta daga ‘yan adawa da jami’an kasar, ya tilasta masa jinkirta kudurin dokar sake yi wa bangaren shari’ar garambawul.

Sai dai masu zanga-zangar sun ce ba jinkirtawa suka bukata daga gare shi ba illa iyaka ya dakatar da kudurin dokar baki daya.

Labarai Masu Nasaba

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Yanke Wa Wasu ‘Yan China 2 Hukuncin Daurin Shekaru 12 A Sakkwato

Next Post

Sabbin Zababbun Gwamnoni Na Bisa Tsinin Mashi

Related

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu
Manyan Labarai

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

27 mins ago
Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo
Labarai

Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

10 hours ago
Gwamnan Bauchi Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP
Manyan Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

16 hours ago
Shanuna Sun Fi Saukin Kiwo A Kan Mulkin Nijeriya – Buhari
Rahotonni

Shanuna Sun Fi Saukin Kiwo A Kan Mulkin Nijeriya – Buhari

18 hours ago
Alhazan Abuja Sun Gamu Da Tasku Sakamakon Rashin Samun Masaukai Masu Kyau A Saudiyya 
Labarai

Za Mu Kwashe Daukacin Maniyyatan Bana 6000 – Hukumar Alhazan Kano

19 hours ago
Ƴan Sanda A Gombe Sun Kama Matasa 11 Da Ake Zargi Da Kalare
Labarai

Ƴan Sanda A Gombe Sun Kama Matasa 11 Da Ake Zargi Da Kalare

21 hours ago
Next Post
Nijeriya

Sabbin Zababbun Gwamnoni Na Bisa Tsinin Mashi

LABARAI MASU NASABA

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Yawan Kyautarsa — Garba Shehu

June 4, 2023
Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

Babu Gaskiya A Labarin Mutuwar Akeredolu -Gwamnatin Ondo

June 3, 2023
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Tsarin Wayewar Kan Kasar Sin Mai Dacewa Da Zamani

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Tsarin Wayewar Kan Kasar Sin Mai Dacewa Da Zamani

June 3, 2023
Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Wuraren Al’adun Sin Tana Da Babbar Ma’ana

Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Wuraren Al’adun Sin Tana Da Babbar Ma’ana

June 3, 2023
Sin Ta Jaddada Kira Ga Sassan Masu Ruwa Da Tsaki A Rikicin Sudan Da Su Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta

Sin Ta Jaddada Kira Ga Sassan Masu Ruwa Da Tsaki A Rikicin Sudan Da Su Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta

June 3, 2023
Rashin Lafiyar Maigidana Ne Babban Tashin Hankalin Da Na Fuskanta A Vila – Aisha Buhari

Rashin Lafiyar Maigidana Ne Babban Tashin Hankalin Da Na Fuskanta A Vila – Aisha Buhari

June 3, 2023
‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Yahaya Bello Hari, Sun Raunata Jami’an Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Yahaya Bello Hari, Sun Raunata Jami’an Tsaro

June 3, 2023
Shugaban Eritrea Da Takwaransa Na Congo Kinshasa Sun Yabawa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Shugaban Eritrea Da Takwaransa Na Congo Kinshasa Sun Yabawa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

June 3, 2023
Wane Ne Sabon Kocin Chelsea Mauricio Po-chettino?

Wane Ne Sabon Kocin Chelsea Mauricio Po-chettino?

June 3, 2023
Sin Ta Yi Tir Da Kalaman Sakataren Tsaron Amurka A Taron Shangri-La

Sin Ta Yi Tir Da Kalaman Sakataren Tsaron Amurka A Taron Shangri-La

June 3, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.