Yanzu haka ana daf da bude baje kolin kasa da kasa na kayayyakin masarufi na kasar Sin, kuma yayin baje kolin na bana, an tsara kafa yankin nune nune mai lakabin “Kewaye biyu na sayayyar kasa da kasa”.
Yayin da duniya ke fuskantar sauye sauye da ba a taba ganin irin su ba a baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmiyar shawara ta “Gina sabon tsarin bunkasa kasa”, mai kunshe da muhimmin jigo wato “kewayawar kasuwar gida da ake dogaro kan ta, da bunkasa hada hadar cikin gida, da ta kasa da kasa, ta yadda sassan za su rika bunkasa juna”. Wannan salo na samar da ci gaba shi ne alkiblar raya tattalin arzikin Sin mai karko.
- Xi Jinping Ya Gana Da Ma Ying-Jeou A Beijing
- Wang Yi Ya Yi Karin Haske Kan Shawarwarin Sin Na Warware Batutuwan Dake Jan Hankulan Sassan Kasa Da Kasa
Baje kolin din na bana, zai hallara kayayyakin kamfanoni har 3000 daga kasashe da yankuna 59, tare da hade kasuwannin Sin da na ketare. Kuma baje kolin muhimmin ginshiki ne na ingiza “Kewaye biyu”, da samar da muhimmin dandali ga kamfanonin kasa da kasa na cin gajiyar kasuwar kasar Sin tare, da kuma kara yayata hajojin kasar Sin ga duniya.
Kasar Sin ta kafa kawancen cinikayya da kasashe har 140, wanda hakan ya sanya ta zama ta daya a duniya, a fannin yawan abokan huldar cinikayyar kayayyaki da hidimomi. Abun tambaya a nan shi ne, ga kamfanonin kasa da kasa, ‘yan kasuwa, da masu sayayya, wane ne ba zai yi sha’awar kyakkyawar makomar “Kewaye biyu na sayayyar kasa da kasa”, da ma bukatun da ake samu daga hakan ba? (Saminu Alhassan)