Shafin TASKIRA shafi ne da yake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, cikin sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi Sadaka, duba da yadda wasu mutanen ke mantawa da amfaninta da kuma mahimmancinta wanda ba sai iya watan ramadana kadai za a rika aiwatarwa ba.
Duk da cewa wasu na son yin sadakar amma ba su san ta yadda za su aiwatar da ita ba, musamman idan aka yi duba da wadanda suke yin sadaka dan wata manufarsu ta daban kamar; fariya, gasa, yabo, neman suna, da dai sauransu, ba domin Allah ba.
Wannan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Fadi mahimmancin sadaka, Wa ya kamata a bawa sadaka?, Fadi hanyoyin yin sadaka”, wacce shawara za a bawa marasa yin sadaka?”.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna:
Muhimmancin sadaka na da yawa baya ga kariya da take yi, sadaka tana hana bambancin da ake yi tsakanin mai kudi da kuma talaka, sadaka tana hada kan al’umma musulmi guri daya, tana taimakawa marayu, masu takaba da manya wadanda suka manyanta wajen nuna musu cewar suma suna da gata, tana kuma kusanto mutum da Allah ta’alla. Wadanda ya kamata a bawa sadaka; Marayu, iyalai masu karamin karfi, masu takaba, ‘yan gudun hijra, dalibai da sauransu. Hanyoyin bada sadaka na da dumbin yawa kamar; bada sadaka ta hanyar bada kudi, yinta ta hanyar dauke abu daga kan hanya wanda zai cutar da dan’Adam, hada kungiya ko kirkirar kungiya ko bada gudunmawa a kungiyar taimakon al’umma, ko bada kaya a madadin yardar su, bada kayan abinci a dafe ko danye da dai sauransu. Shawara ga marasa yin sada shi ne su rinka yi da kadan-kadan domin kuwa sadaka ba ta yin yawa ba ta kadan, komai kankantar sadakar da kayi sadaka ce indai har da zuciya da ka bada ita, sannan su san amfanin sadaka, su san hanyoyin sadaka.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya muhimmancin sadaka a rayuwar dan’adam musamman musulmi tana da yawa, musamman sadakar da aka yi domin Allah, domin tana taimakawa wajen karbar addu’a, kawar da masifu dama karin budi a fannoni da dama na rayuwa don haka muhimmancin sadaka ya fi gaban kidayawa. To magana ta gaskiya wadanda ya kamata a bawa sadaka sunada yawa ,kamar; maskinai, masu karamin karfi, matafiya dama ‘yan’uwa makusanta. To hanyoyin yin sadaka sunada dama kamar; ciyarwa, samar da ruwan sha, rabawa al’umma kudi ko kayan abinci dama fadawa mutane kyakkyawar magana domin ita ma sadaka ce, don sadaka tana da nau’oi da yawa. To magana ta gaskiya kin yin sadaka ga masu hali tamkar tauye Kai ne, domin yin sadaka taimakon kai ne, domin ita sadaka tana bude kofofin alkairai da dama ga masu yin ta, don haka ya kamata mu daure mu rika yin sadaka daidai karfin mu domin za ta zama budi a gare mu, Allah ya bamu ikon yin sadaka domin Allah.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA:
Tana maganin Masifa da wani iftila’ in da bai zo wa bawa ba.
Muskinai musamman wadanda ba su da lafiyar da za su iya neman na kansu wadanda sai an taimaka musu ko sun fito bara suke samun abin da za su ci. Hanyoyin yinta suna da yawa amma wacce Allah ya fi so ita ce; wadda za ka yi da hannun dama hagun ba ta sani ba. Gaskiya shawarata a gare su su daure su rika ko babu yawa kuma ayi ta domin Allah badon ayi a burge wasu ba, sabida koda ayyukan da mamaci yake mora bayan mutuwarsa akwai sadaka a cikinsu to kun ga kuwa ita sadaka ba karamin aikin lada bace gaskiya. Allah ya sa mu dace.
Sunana Muhammad Isah Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Sadaka magani ce, waraka ce, kuma kariya ce daga dukkan cututtuka Sadaka garkuwa ce daga sharrin arayi, ko gobara, da dai sauran su. Sadaka na daya daga samun sauki da waraka daga cuta ko wacce irin matsala. A cikin hadisin manzon Allah (S.A.W) an ambaci cewa; sadaka na iya kawar da bala’i kuma tana warkar da cututtuka. Shawara idan mutum yana sadaka tana hana bala’i, sadaka na jawo albarka, sadaka na tsarkake rai da kuma dukiya, sadaka nasa Allah ya saukaka wa mutum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp