Assalamu alaikum iyaye sannunmu da sake haduwa cikin filin mu mai far in jini RAINO DA TARBIYYA.
A yau filin namu zai yi tsokaci ne a kan koya wa yara dogaro da kai ta hanyar sana’a. Yana da kyau bayan yara sun dawo makaranta ya kasance akwai wata sana’a da suke yi wanda za su taimaki kansu har su taimaki iyayensu a gaba. Barin yara ba tare da abinyi ba hatsari ne mai girman gaske.
Wasu iyaye kan yi kuskuren kyale yaro ya yi ta rayuwa a haka ba tare da an koya masa fafutukar neman na kai ba wanda hakan ba daidai ba ne kuma ba gata ba ne.
Akwai kanana sana’o’i na cikin gida wanda ba lallai yaro sai ya fita talla ba a gida ma za a zo a saya.
Iyaye mu dauki nuna wa yaro dogaro da kai ta hanyar sana’a da muhimmanci saboda halin rayuwa, akwai mutuwa fa!. Sai kuga wasu yaran in iyaye sun rasu sun barsu ba sana’a sai su tagayyara wani lokaci har su lalace saboda rashin kudi.
Sana’a tana da rana da kuma rufa asiri. Idan yaro na sana’a iyaye kan huta da tambayar kudin kitso ga mace ko kudin aski ga yaro namiji.
Yana kuma kawar da hankalin yaro ga fadawa hanyar lalacewa don yana da abin yi.
Allah ya bamu ikon koya musu sana’a don dogaro da kansu.