Mujallar Qiushi ta kasar Sin za ta wallafi jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping gobe Jumma’a 1 ga watan Agusta, wanda Xi ya taba gabatarwa a gun babban taron kiyaye muhallin halittu na kasar Sin a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2023.
Jawabin ya bayyana cewa, bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin ta riga ta shiga sabon mataki na neman samun ci gaba mai inganci, wanda ke bukatar gaggauta kiyaye muhallin halittu da rage yawan iskar Carbon da ake fitarwa. Aikin kiyaye muhallin halittu na fuskantar matsin lamba. Ya kamata a yi kokarin zamanantar da kasar Sin bisa tushen samun daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. (Kande Gao)