Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Caroline Wura-Ola Adepoju, ta sanar da kafa dokar ta-baci kan batutuwan da suka shafi fasfo a kasar nan.
Ta bayyana hakan ne a ziyarar aiki da ta kai jihar Legas a ranar 15 ga watan Yuni 2023, inda ta jaddada bukatar gaggawa ta magance kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta wajen samun fasfo tare da ayyana cikakken shirin daukar matakin da ya dace domin tunkarar wadannan matsaloli yadda ya kamata.
Ziyarar ta Ag CGI a Legas ta kunshi nazarin muhimman al’amura da suka shafi gyara matsalar Fasfo. Ta kuma kaddamar da wani katafaren ofishin biza na zamani a babban zauren isowar baki a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Mohammed, inda ta nuna kudirinta na inganta harkokin shige da fice baki daya ga masu shigowa Nijeriya. Bayan haka ta kai ziyarar bazata zuwa ofishin fasfo na Alausa domin gane wa idonta halin da ake ciki.
A cikin jawabinta, Ag. CGI Adepoju ta jaddada wajabcin wargaza duk wasu abubuwa da ke kawo cikas wajen neman Fasfo. Ta kuma jaddada cewa, manyan jami’an NIS sun himmatu sosai wajen magance matsalolin da suka shafi fasaha don tabbatar da samar da ingantaccen aiki ga jama’a.
Bisa la’akari da muhimmancin wayar da kan jama’a game da sauran masu ruwa da tsaki musamman sarakunan gargajiya, mukaddashiyar shugabar ta NIS ta fara wannan yunkurin ne da wata ziyara da ta kai wa Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, inda ta nemi hadin kan sarakunan gargajiya wajen wayar da kan jama’a game da illolin da ke tattare da safarar mutane da kuma kaddamar da hadin gwiwar yaki da wannan matsala.
Dokar ta-baci kan batutuwan fasfo na nuni da sabon alkawarin da NIS ta yi na magance kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta na neman fasfo.
Idan za a yi tunawa, Ag. CGI Adepoju kwanan baya ta umurci dukkan jami’an da ke kula da fasfo, da sassan da abin ya shafa da kuma ma’aikatan NIS ciki har da Ofishoshin Jakadancin Nijeriya a kasashen waje, da su yi aiki tukuru domin kawar da duk wani cikas da ke hana ‘yan Nijeriya samun fasfo cikin gaggawa. Hukumar NIS tana yin amfani da fasaha tare da ƙaddamar da ingantattun matakan gudanarwa don haɓaka aikace-aikacen Fasfo da tsarin bayarwa.
Mukaddashiyar shugabar ta bukaci daukacin ‘yan Nijeriya da su ci gaba da hakuri tare da bayar da hadin kai ga hukumar ta NIS yayin da take daukar kwararan matakai don magance matsalar Fasfo. Ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa ana kokarin ganin duk wani dan Nijeriya da ya cancanta ya samu Fasfo a kan lokaci.