Aƙalla mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie-Badeggi, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa motar ɗauke da hatsi ta gwamnatin tarayya ce, kuma fasinjojinta maza ne kimanin 36, daga Legas zuwa Kano.
- Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato
- An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A Nasarawa
Hatsarin ya faru ne da ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, lokacin da direban ya yi ƙoƙarin ƙetare wani ɓangare mara kyau na hanyar da ake ginawa.
Daraktan hukumar kula da sufuri na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana kan aikin ceto da binciken kan iftila’in.














