Wani mummunar hatsarin mota ya ci rayukan mutum 18 a gadar Isara da ke kusa da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Asabar.
Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Jami’in watsa labarai na FRSC, Bisi Kazeem, ya shaida ta cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi cewa, “Daga rahoton binciken hadarin da ya faru da ya rutsa da motoci guda uku dauke da fasinjoji 25 da suka kunshi maza 6 manya, babbar mace guda, yaro karami, da wasu mutum 17 da ba iya gano yanayinsu ba sun kone kurmus ba tare da ana iya ganesu ba.
“Daga cikin wannan adadin, mutum 18 sun mutu, sauran bakwai din kuma sun gamu da munanan raunuka da suka hada da manyan maza biyar, babbar mace guda da karamin yaro.”
Ya kara da cewa, binciken ya nuna cewa musabbabin hadarin da ya kunshi motoci kirar Mazda biyu da Previa bus shine gudun wuce sa’a da kuma karya dokokin tuki.
Kazalika, sanarwar ta ce Babban Shugaban Hukumar ta FRSC, Dakta Boboye Oyeyemi, ya gargadi direbobi da su rika kokarin kauce wa tukin dare, tare da jawo hankalinsu su bi ka’idojin tuki a kowani lokaci domin kiyaye rayukansu da na fasinjojin da suke dibowa.
Da yake magana dangane da jerin hadarin ababen hawa da suka auku da karfe 10:20 na daren ranar Asabar a kusa da gadar Isara (KM 61-750) da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya rutsa da su.