Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya Janar Lucky Irabor ya bayyana cewa, Jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kai hari a Jihar Kano, “wanda ka iya zama mafi muni a Tarihin Kasar”.
Janar Irabor wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da ake tattaunawa da shi cikin wani shiri kan Ranar Dimokuradiyya a kafar talabijin ta Channels TV, ya ce an dakile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari a cocin garin Owo ta Jihar Ondo, wanda ‘yan bindiga suka bude wa masu ibada wuta tare da kashe mutum fiye da 40.
“Babu mamaki ba ku da labari cewa a makon da ya wuce kadai da aka kai harin coci a Owo, a Kano misali, mun yi nasarar dakile harin da ka iya zama mafi muni a kasar nan tamu saboda bayanan sirri da muka samu,” in ji shi.
“A wannan aikin, mun gano kayayyakin da ake hafa abubuwan fashewa da su. Mun kwace kunshin makamai masu yawan gaske da ‘yan ta’ada ke kokarin yin amfani da su a sassan kasar nan, har da Abuja.”
Janar Irabor ya kara da cewa an samu karin tsaro a Kasar acikin Shekara Daya da ta gabata fiye da shekarun baya