Gwamnan jihar Adamawa Ahamdu Umaru Fintiri, ya nuna damuwa game da karuwar ayyukan yara ‘yan shila a Yola, babban birnin jihar, inda ya dora alhakin matsalar kan iyayen yaran.
Da take magana a madadin gwamnan, mataimakiyar gwamnan jihar Farfesa Kaletapwa Farauta, ta ce kamata yayi iyaye su sa ido kan harkokin yaransu na yau da kullum, domin nauyi ne da Allah zai tambayesu a ranar gobe.
- Yansanda Sun Kama Mutum 6 Bisa Zargin Satar Keke-napep Uku A Adamawa
- Ministan Harkokin Kasar Wajen Kasar Sin Da Takwaransa Na Iran Sun Tattauna Ta Wayar Tarho Kan Rikicin Isra’ila Da Iran
Ta ci gaba da cewa “a madadin gwamna Ahamdu Umaru Fintiri, muna rokon iyayen yara da su rika tura yaransu cibiyoyin koyon sana’o’in dogaro da kai, da zai taimakawa yaran su samu sana’ar da za su dogara da kansu kuma su samu tallafin gwamnatin bayan sun koyi sana’ar da ransu yake so.
“Haka ya kamata, maimakon su rika aikata munanan yyukan da wata rana zai kaisu ga rasa rayukansu, bai Kamata ba, iyaye su gargadi yaransu domin su ne shugabannin gobe” inji Farauta.
A nasa jawabin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Yahya Nguroji, ya ce, rundunar ta dauki tsauraran matakai kan yaran inda ya ce, rundunar ta kame yara ‘yan Shila fiye da 100, ta kuma gurfanar da su a gaban kotu.