Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce, ta kama wasu mutane shida da ake zargi da satar Keke-napep a jihar Adamawa.
Wadanda ake zargin sun hada da Idi Abdullahi, Mohammad Tukur, Umar Hassan, Umar Yusha’u, Usman Ladan da Abubakar Idrisa.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 3 Da Ake Zargi Da Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane A Bauchi
- Takaicin Fyaden Kananan Yara Ya Sa Na Shirya Fim Din AKASI – Yakubu Gwammaja
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Yahaya, ya ce, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Talla
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Dankombo Morris ya yaba da kokarin da jami’ansa masu yaki da ayyukan ‘yan kungiyar “Shilla” suka yi na cafke wadanda ake zargin.
Talla