Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL) Mele Kyari, ya bayyana cewa coci-coci da masallatai da jami’an tsaro da kuma al’ummomin da bututun mai ya bi ta yankin su, duk suna da hannu wajen fasa bututun man fetur.
Ya bayyana hakan ne ayau Talata a wajen taron tattaunawa na mako-mako da kungiyar manema labarai na fadar shugaban Kasa ke shirya wa a fadar gwamnati dake Abuja.
Ya ce: “Kamar yadda ku ma kun sani, akwai munanan ayyukan masu fasa manyan bututun mu tun daga Atlas Cove har zuwa Ibadan, sannan da kuma duk wasu dakunan ajiya (Depot) guda 37 da muke da su a fadin kasar nan. Dukkansu babu wanda za a iya tura mai ta cikinsa ayau.
“Kuma kowa yasan meyasa bama turawa, yau shekara 15 kenan, Bututunmu na Warri zuwa Benin ba mu yi amfani da shi ba. Kowanne digon Mai daya muka tura sai ya bace. Kuma ba shakka, za ku tuna abin bakin ciki da lamarin gobara ya afku a kusa da Warri, kusa da Sapele wanda ya kashe mutane da dama.
“Akwanakin baya, a wani yanki a Legas, Lokacin da gobara ta tashi a daya daga cikin bututunmu, mun gano cewa ana satar man daga cikin gidaje da Masallatai da Coci-coci.
“Hakan yana nufin kowa yana sane da satar man. Babu yadda za a yi a kwashi mai cikin Tanka a cikin unguwannin Jama’a amma ace ba a gani ba.”