Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa ta kammala nazari kan sakamakon zaben gwamnoni da aka gudanar a ranar a Asabar da ta gabata a jihohi 28.
A cewar hukumar, ta kuma kammala nazari kan sakamakon gwamnoni a jihohin Abiya da Inugu, inda tun da farko ta dakatar da tattara sakamakon zaben da aka yi da kuma tashe-tashen hankula.
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Equatorial Guinea
- An Yanke Wa Wasu Mutane 4 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Legas
Mai Magana da yawun hukumar INEC, Festus Okaye ya bayyaba hakan ne a ranar Laraba a Abuja.
Hukumar ta tunatar da cewa ta yi taro ne a ranar Litinin 20 ga watan Maris, inda ta sake duba yadda zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi suka gudana a fadin kasar ranar Asabar 18 ga watan Maris.
“Sakamakon taron, hukumar ta dauki matakin dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a wasu sassan jihohin Abiya da Inugu, domin gudanar da nazari kan yadda ake tattara sakamakon zaben a jihohin biyu.
“Hukumar ta kammala bitar. Sakamakon haka ne ta bayar da umarni a ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihohin Abiya da Inugu a ranar 22 ga watan Maris.
“Hukumar ta yaba da hakuri da fahimta da mutanen jihohin biyu suka nuna yayin da muke kammala ayyukan hada-hadar.”