Dakarun da ke ƙarƙashin Atisayen haɗin kai sun hallaka sama da ’yan ta’adda 70, ciki har da manyan shugabanninsu guda uku, a yayin wani hari a wuraren da ake kira Timbuktu Triangle a Arewa Maso Gabas.
Bayanin ya nuna cewa an gudanar da wannan aiki ne ta hanyar haɗin gwuiwar jiragen sama da Sojojin ƙasa, inda aka tarwatsa sansanonin ’yan ta’addan a jihohin Borno da Yobe. A ranar Juma’a, dakarun suka ƙaddamar da farmaki a kan wata maɓoyar masu ikirarin jihadi da ke tsakanin jihohin biyu.
- Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda, Sun Kama Masu Safarar Makamai, Sun Ceto Mutane
- Kwanaki Bayan Kashe Masunta 20, Boko Haram Ta Kashe Sojoji 20 A Borno
A yayin wannan artabu, babban jami’in tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya bayyana cewa sojoji 22 sun rasa rayukansu, ba kamar rahoton farko da ya nuna 27 ba.
Haka kuma, dakarun sun kashe Talha, shugaban ’yan ta’adda na musamman, da Malam Umar, kwamandan ayyukansu, da Abu Yazeed, kwamandan rundunar ’yan ta’addan.
Buba ya ƙara da cewa ’yan ta’addan sun yi amfani da abubuwan fashewa (IEDs) don daƙile hari daga dakarun, amma hakan bai hana nasarar dakarun ba wajen fatattakar su daga maɓoyar su ba.