Shahararren mai wasan barkwanci a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Bashir Bala wanda aka fi sani da Chiroki.
A wata hira da ya yi a jarumar Kannywood Hadiza Gabon a cikin shirinta na ‘Gabon Room Talk Show’, ya bayyana yadda suka yi gwagwarmaya domin masana’antar ta zama abin da ta zama a yanzu.
- Dabarun Samun Kudi Ga Matan Aure Ta Hanyar Fasahar Sadarwa – Hajiya Hafsat
- Yadda Wasu ‘Yan Mata Ke Yawan Kai Ziyara Wurin Saurayi Da Gidan Surukai
Da ake tambayar shi banbancin Kannywood a da da yanzu Chiroki ya bayyana cewar a lokacin da suka yi zamani a masana’antar babu yawan jarumai kamar yanzu.
Yanzu Kannywood ta tsaya da kafafunta ta zama babbar masana’anta da fiye da mutum dubu ashirin suke cin abinci a cikinta, ba kamar a namu lokacin ba da ba mu fi mutum dubu daya ba.
A wancan lokacin mun sha duka da zagi sakamakon rashin fahimtar mu da mutane suka yi, inda suke ganin cewar mun shigo da wani sabon abu na yahudawa da basu saba ganin sa ba.
Ba kamar yanzu da kai ya waye ba har ake saka fina-finai a yanar gizo da sauran wurare da mutane ke biyan kudade su kalla.
Daga karshe Chiroki ya bukaci manyan mahukuntan masana’antar na yanzu da su dinga bai wa matasa masu hazaka da baiwa damar nuna baiwarsu ba wai ace dole sai wanda aka saba dashi ko kuma wanda bai iya ba, idan dai mutum nada gudunmawar da zai iya bayarwa to ta kamata a bashi dama a Kannywood.