Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da shirin gwamnatinsa na ƙirkiro da sabbin masarautun gargajiya bisa hujjar ƙarin buƙatar hakan daga ɓangarorin al’ummomin jihar da dama.
Gwamna Fintiri ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙabilar Heba daga ƙaramar hukumar Hong, ya ce nan ba da jimawa ba zai aika da ƙudirin dokar ƙirkiro masarautun ga majalisar dokokin jihar domin ya zama doka.
- Rundunar ‘Yansanda Ta Ɗaukaka Matsayin Jami’anta 12 A Adamawa
- Adamawa Za Ta Kashe Naira Biliyan N8.1 Don Gina Gadoji
Ya ci gaba da cewa “ina so in tabbatar muku da cewa gwamnati za ta yi nazari kan bukatar ku na ta amince ko akasin haka, kuma idan muka gano akwai buƙatar mu samar da masarautar Heba ba za mu yi ƙasa a gwuiwa ba wajen aika ƙudiri ga majalisar dokoki.
“Amma za mu tabbatar da cewa an bi ƙa’ida ta doka, sannan ta zama doka ta kuma ba ku abin da shi ne na ku, domin duk jihar ta mu ce, kuma jihar a yau, babu wanda ya isa ya ɗauka na ƙashin kansa ba, kuma bai kamata mu sami mafari ba” inji Fintiri.
Ya ce
“ta hanyar shirin, Fintiri Business Wallet za mu tallafa wa mata da matasa dubu 60, haka kuma shirin na da nufin shigar da Naira biliyan uku a cikin tattalin arzikin jihar, don ba wa mazauna jihar damar inganta sana’o’in dogaro da kai, da bunkasa tattalin arziki”
ya jaddada.