Ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP Injiniya Nura Khalil ya bayyana cewa sun shirya korar jami’yyar APC daga mulki a zaɓe mai zuwa saboda yadda gwamnati ta ƙksa yin abin azo a gani a shekaru takwas da ta kwashe tana shugabanci
Nura Khalil ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake ƙaddamar da gangamin yakin neman zaɓen sa a ƙaramar hukumar Mashi ta jihar Katsina.
Injiniya wanda ya ce yanzu jihar Katsina bata da sauran komi na ƙaddara, bata da gidaje bata da filaye komi ya kare, ya ce bai taɓa ganin mutane masu ɓarna ba kamar wannan gwamnati.
Ya kara da cewa jihar Katsina na neman mutum da yasan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da za a yi jihar aikin cigaba saboda yadda aka naƙasata a mulkin ‘yan bani na iya.
Haka kuma bayyana cewa dalilin da yasa ya fara wannan yakin neman zaɓen sa a ƙaramar hukumar Mashi shi ne, suna da wani sirri wanda su da Daurawa a jihar Jigawa da kuma Kankia ke da tataccen hasken rana da zai iya samar da haske wuta mai karfin ‘Megawat’ 1,000
“Idan na samu nasarar lashe zaɓe zan yi amfani da wannan damar wajan samarwa jihar Katsina kuɗin shiga kimanin biliyan 100 duk shekara kuma cikin shekaru huɗu zuwa biyar za su iya kaiwa biliyan 4 ko fiye da haka ta hanyar hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana” inji shi
A cewar sa idan aka samu nasarar yin aiki hakan zai ba jihar Katsina damar yin gogayya da jihohi irinsu Kano da kuma Legas da fuskar kasuwanci da sauran sha’anin tattalin arziki da noma da kuma tsaro baki ɗaya.
Injiniya Nura Khalil da ya juya akan batun zaɓe ya ja hankalin matasa da su tabbatar sun zaɓi jam’iyyar NNPP domin samun mafita a wannan rayuwa da ta zama ba tabbas a ƙarƙashin mulkin APC
Yana mai kira ga mata waɗanda ake yaudara ana karɓar katin zaɓen su, da sunan za a ba su Naira dubu 10 zuwa ashirin, wanda ya ce daga ƙarshe ɗari biyar ake ba su.
“mata kuma da rawar da zaku taka wajan ganin jami’yyar NNPP ta samu nasarar lashe zaɓe daga sama har ƙasa ta hanyar tabbatar da cewa an zaɓi jam’iyyar mai alama kayan marmari.
Daga ƙarshe ya yi kira da a zaɓi injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin shugaban ƙasa sannan a zaɓi sauran’yan takarar jam’iyyar NNPP a dukkanin matakai domin warware matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa da Najeriya baki ɗaya.
Shi ma nasa jawabin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya samu wakilcin ɗan takarar gwamna na jihar Kano Abba Gida Gida ya ce zaɓen jami’yyar NNPP a dukkan matakai shi zai yi maganin matsalolin da ake fama da su.
Abba ya nuna jin daɗin sa da irin tarɓa da karancin da aka nuna masu musamman magoya bayan jami’yyar NNPP na jihar Katsina da suka farin ɗango domin halartar wannan gangami a garin Mashi na jihar Katsina.
Ya yi addu’a da fatan cewa jama’a za su fito kwanso da kwarkwata ranar zaɓe domin kawar da jam’iyyar APC da suka addabi al’umma.