Ƙungiyar Izala ta tara sama da miliyan ɗari da saba’in (N170,974,512.50) sakamakon fatun layyan data gabata.
Bayanin hakan ya fito ne daga Bakin Shugaban Kungiyar Izala na Kasa Sheikh Bala Lau , a zantawarsa da manema labarai Jim kadan Baya ya karɓi sakamakon kwamitin tattara fatun layya na wannan shekarar wanda shugaban kwamitin Malam Lamara Azare da Yan majalisar sa suka gabatar.
- Matsalar Ciwon Kwakwalwa A Gidajen Yarin Kasar Nan
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Arokodare Ya Farfaɗo Da Mafarkin Nijeriya A Wasan Rwanda
Taron Wanda aka gudanar da shi a dakin taro na Kungiyar Jama’atu Nasarul Islam dake Kaduna.
Shugaban yace jihar Kaduna itace akan gaba daga cikin jihohi 36 da Birnin tarayya Abuja wajen tara kudin fatun layya Wanda ta tara Naira miliyan 23 sai jihar Kebbi wacce tazo ta biyu da Naira milliyan 21 sai kuma jihar Sakkwato wacce tazo ta uku.
Yace kudadan da aka tara za’ayi amfani dasu wajen ci gaba da aiwatar da Ayyukan Jami’ar musulunci mallakin kungiyar dake Hadejia a jihar Jigawa wacce ake kan ginawa.
Yace irin Wannan sadaka da alumma suke bayarwa zasu tabbatar da cewa anyi amfani da su yadda ya kamata musamman ginin Jami’ar mallakar kungiyar da wasu bangarori domin ciyar da addinin musulunci gaba.
Da yake bayani akan taron da kungiyar ta gudanar a jihar Kaduna dangane da littafin rayuwar Marigayi Abubakar Mahmoud Gumi, yace ya jinjinawa marubucin Dakta Ibrahim Jalo Jalingo.
Akan hakan ya bukaci daukacin Al’ummar kasar da su dage wajen gudanar da addu’oin samun zaman lafiya da kuma magance matsalar tsaro da ya addabi alumma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp