Rundunar sojin Nijeriya ta yaye sojoji 5,800 a kokarinta na magance kalubalen tsaro da ya addabi kasar.
Jami’an dai na cikin jami’an soji Kashi na 82 da hukumar sojin ta ya ye na Depot da ke Zariya a Jihar Kaduna a ranar Asabar.
Da yake jawabi yayin kaddamar da faretin, babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin karfafa kwazon aiki da kuma kara karfin rundunar sojojin Nijeriya.
Ya bukaci sabbin sojin da su yi aiki da kwarewa sosai wacce suka samu kuma su kasance jakadu nagari na Sojojin Nijeriya.
Yahaya ya bukaci sabbin sojojin da su yi amfani da kaifin tunani, jiki da dabi’u da suka samu a yayin horar dasu a ‘yan watannin da suka gabata, ya kuma buka ce su da suyi aiki tukuru a duk inda aka ajiye su domin wanzar da zaman lafiya.