Wani dan kasuwar man fetur mai zaman kansa Mike Osatuyi, ya ce farashin litar mai na adalci shi ne kawai tsakanin Naira N200 zuwa N210 a kowace lita.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Legas, inda ya ce, tsarin farashin na Gwamnatin Tarayya wanda ya kayyade farashin litar man fetur a kan N169 bai dace ba kuma hankali ba zai dauka ba, sabida, daga wurin dakon man zuwa gidajen man fetur, kowacce lita tana zuwa a kan Naira N194 bayan biyan kudin harajin kungiya da sauransu.
“Ina sayen man fetur a kan N186.50k kan kowace lita daga ma’ajiyar main fetur ta gwamnati sannan kuma ina kashe kimanin naira N9.50k kan kowacce lita daya akan harajin kungiya da sauransu.
“Ta yaya zan iya sayar da man akan Naira N169 a kowace lita bayan na ci karo da karin kudi a hanya?” ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN.
“Babu wani dan kasuwa da zai iya siyar da man fetur a kan kayyadadden farashin Naira 169 a kan kowace lita a halin yanzu, idan dai man zai zo gidan man a kan Naira N194 kan kowace lita.
Wakilin NAN da ya sa ido a gidajen mai a Legas ya ruwaito cewa galibin gidajen mai na ‘yan kasuwa masu zaman kansu suna sayar da mai a tsakanin N180 zuwa N200 kan kowace lita.
Manyan ’yan kasuwar da ke sayar da man fetur kan farashin Naira N169 a kan kowace lita na da dogayen layi, kamar yadda wakilin ya ruwaito.