Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya na alfahari da Dangote kan yadda yake inganta tattalin arzikin kasar nan.
A jiya ne kamfanin Dangote ya samu gagarumar lambar yabo daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bayyana matsayin gwamnati kan ci gaban da kamfanin ya samu a Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.
- Jikar Dantata Ta Rasu Tana Da Shekaru 40 A Duniya
- Nijeriya Ta Yi Nasara A Kotun Ingila Kan Rikicinta Da Kamfanin P&ID
Amincewa da shugabancin ya zo ne bayan karramawa da lambobin yabo da kamfanin ya samu don samar da dubban ayyukan yi da kuma mai tasiri ga tattalin arzikin Nijeriya.
Shugaba Tinubu wanda ya halarci taron tattalin arzikin Nijeriya karo na 29 da ke gudana a Abuja, ya ce: “Kuna da tasiri. Ku ci gaba da yin kyawawan abubuwan da kuke yi. Ku ci gaba da saka hannun jari a Nijeriya.”
Dangote shi ne babban mai daukar ma’aikata bayan gwamnati, kuma daya daga cikin manyan masu hannu da shuni a nahiyar.
A jawabin da ya gabatar tun farko lokacin da yake bude taron shekara-shekarar, shugaban ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su shiga sahun masu dawo da ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, inda ya kara da cewa kasar za ta iya bunkasa ne ta hanyar hadin gwiwa.
Masana da suka yi jawabi a wajen taron sun bayyana cewa Nijeriya na jiran matatar man fetur ta Dangote, inda suka bayyana kwarin gwiwar cewa hakan zai kawo wani gagarumin ci gaba ga tattalin arzikin kasar nan.
Da yake jawabi a wajen taron mai taken: ‘Bude Hanyar Yaki Da Cin Hanci da Rashawa’, Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin Dangote Industries Limited, Mista Olakunle Alake, ya ce ya yi farin ciki da yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ta fahimci rawar da kamfanoni ke takawa, tare da karfafa bukatar hadin gwiwa.
Mista Alake ya ce dole ne Nijeriya ta bunkasa tattalin arzikinta musamman bangaren masana’antu domin samun damar taka muhimmiyar rawa a yankin Afirka da bangaren ciniki (AFCFTA).
Ya ce duk da cewa AFCFTA ba ita ce mafita ga tattalin arzikin Nijeriya ba, amma ya yi watsi da cewa kasar nan za ta iya samun tagomashi daga gare ta ta hanyar tallafawa ci gaban masana’antu.
Mista Alake ya bukaci gwamnatocin kasashen Afirka ta Yamma da su gyara matsalolin da ke kawo cikas ga aiwatar da ka’idojin kungiyar ECOWAS, inda ya bayyana cewa har yanzu harkokin kasuwanci a kasashen yammacin Afirka na samun koma baya.
Ya bayar da shawarar inganta iyakokin, tashoshin jiragen ruwa a nahiyar domin samun bunkasar tattalin arziki.