Kungiyar MalamJami’oi ta kasa (ASUU), ta soki wasu ministocin Shugaba Muhammadu Buhari bisa fadar karya a yayin da ake tattaunawa da su.
Kungiyar ta nuna takaicinta kan karyar da Ministan Ilimi Adamu Adamu da takwaransa na Kwadago da ayyuka Chris Ngige da kuma karamin ministan Kwadago Festus Keyamo SAN suka furta kan abinda ya shafi bukatun malaman.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar jim kadan bayan kammala taron shugabannin zartarwa na kungiyar da ya gudana a Abuja don yin nazari kan cigaba da yajin aikin da Kungiyar ke yi. Wanda yanzu hakan kungiyar Malaman ta kara wa’adin Watanni hudu, Wanda zai fara daga ranar 1 ga watan Augustan 2022.
Ta ce, gwamnatin Tarayya ta yaudare su ta hanyoyi da dama kan tattaunawa don samun kyakkyawar fahimta tsakaninta da gwamnatin akan yajin aikin kungiyar.
ASUU ta soki Ngige da Keyamo kan zargin fadan ba daidaiba, kan cewa, Gwamnatin Tarayya na bukatar naira tiriliyan 1.1 don ta biya bukatun da kungiyar ta bijiro da su na karin Albashi.
ASUU ta ce, ta yi mamaki kan yadda Chris Ngige Festus Keyamo da sauran hukumomin Gwamnatin Tarayya suka furta wannan adadin kudaden, naira tiriliyan 1.1 a matsayin kudaden da kungiyar ke bukata don biyan Albashim, “wannan Maganar sam ba haka take ba”.