Kimi K3 Ya Bayyana Yunkurin Sin Na Raya Fasahar AI A Bayyane Ta Yadda Kowa Zai Amfana
An kaddamar da Kimi K3, wani samfurin kirkirrarriyar basira ta AI da kamfanin Moonshot AI na kasar Sin ya samar, a ranar Juma’ar da ta gabata, wanda ya zama wata sabuwar nasara a fannin raya AI mai budadden tsari. A cewar kamfanin Moonshot AI, Kimi K3 mai kididdigar koyo triliyan 2.8, ya zama samufurin AI mai budadden tsari mafi girma a duniya. Haka kuma, samfurin ya nuna matukar kwazo a fannonin nazari da dama, inda ya zama cikin tsare-tsaren AI da ke kan gaba a duniya. Sa’o’i kalilan bayan fitar da shi, Kimi K3 ya kai matsayi na 1 cikin jerin AI mafiya inganci na Arena Rankings, inda ta zama fasahar AI ta kasar Sin ta farko da ta kai matsayi na 1 a dandalin mai tasiri. Masu nazari a masana’antar AI sun ce wannan nasara ba ci gaban fasaha kadai take nunawa ba, har da karuwar rawar da bayyana komai ke takawa da hadin gwiwa da samar da muhallin raya makomar fasahar AI a duniya. (Fa’iza Mustapha)



















