Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce yana ci gaba da buga sababbin takarkun kudi, sai dai har yanzu ‘yan Nijeriya na kokowa da cewa, suna ci gaba da fuskantar matsala wajen samun takardun kudin.
Wannan batu dai ya sake kunno kai ne a daidai lokacin da wasu ‘yan Nijeriya ke ci gaba da yin korafe-korafe a game da yadda ba sa iya samun adadin takardun kudin da suke bukata a zahiri a bankunan kasuwancin baya ga matsalar na’ura da sabis mai inganci wajen tura ko karbar kudi ta Intanet ko manhajojin bankunan da ake yawaitar fama da su.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Kasar Sin Ba Ita Ce Tushen Saka Wa Kasashen Afirka Tarkon Bashi Ba
- An Kama ‘Yansanda Biyar Da Dan Kasuwa A Filato
A bayaninsa CBN, ta bakin darakta mai lura da harkokin bankuna na bankin, Malam Haruna Bala Mustapha, ya ce bankin na ci gaba da buga sabbin takardun kudi tare da rarraba tsoffin kudin don a samu wadata a kasar nan, yana mai cewa wasu ‘yan kasar nan idan suka samu sabbin tsakardun kudi suna ajiyewa ne don gudun abun da ka je ya dawo nan gaba kuma nan ba da jimawa ba za a samu saukin al’amarin sossai.
Idan ana iya tunawa dai a ranar 3 ga watan Maris ne kotun koli, ta yanke hukuncin tsawaita wa’adin amfani da takardun Naira 200, 500 da kuma 1000 zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023 bayan kwan-gaba kwan-baya da aka yi ta samu da matakin janye tsoffin takardun kudin daga cikin al’umma tun karshen watan Janairu, lamarin da ya jefa mutane cikin matsin rayuwa.