Ƙungiyar Matasan Arewa ta bayyana amincewa da shugabancin Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), tare da jaddada cewa ƙungiyar ta shirya tsaf domin samar da zaman lafiya, haɗin kai da samar da wadata a faɗin Arewacin Nijeriya baki ɗaya bisa ingantaccen tsari.
Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa da kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyoyin matasan Arewa (JACOM), sun yi amanna da ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) domin ganin an samu sauyi tare da sauya akalar shugabancin ƙungiyar ta fannin zamantakewa da al’adun Arewacin Nijeriya.
- Manoma 40,000 Za Su Amfana Da Takin Zamani Na Bunkasa Noman Rani A Filato
- Shirin Mati A Zazzau’ Zai Zama Fim Na Hausa Na Farko Da Za A Haska A Tashar Netflix
Ƙungiyar Matasan Arewar, a wata sanarwa da Shugaban JACOM, Murtala Abubakar da Sakatarenta, Israel Musa suka fitar ta bayyana cewa ci gaban da ƙungiyar ta ACF ta yi ya kankama ne a makon da ya gabata, yayin ƙaddamar da sabon kwamitin zartarwa na ƙasa don gudanar da harkokin ƙungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa bayan ƙarewar wa’adin Tsohon Ministan Noma, Dattijo Audu Ogbe.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “sauyin da aka samu cikin kwanciyar hankali da lumana ya biyo bayan yunƙurin da kwamitin zaɓe wanda ya samar da ƙungiyar zartaswa a halin yanzu a ƙarƙashin jagorancin Mamman Mike Osman SAN, shaida ce a sarari ga jajircewar ACF na tunkarar nauyin da ke kanta da sabbin dabaru da fa’idoji.
“A yayin da muke sa ido kan manufofin shugabanci na yankin Arewa a halin yanzu, ƙungiyarmu ta tabbatar wa ACF cikakken jajircewarmu da ɗaukacin al’ummar Arewacin ƙasar nan a shirye muke mu hada kai da sabon kwamitin zartarwa na ACF ba wai don tabbatar da hadin kai ba kawai, amma sai don ƙara wa matasa himma da hikimar don tunkarar ƙalubale, sannna kuma don dawo da tsaro, zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a yankinmu don fatan alheri da kuma don gobe, musamman a wannan mawuyacin lokaci.
“Muna kira ga ɗaukacin ‘yan Arewa ba tare da la’akari da harshe, addini, tsatson ko siyasa ba da su haɗa kai su baiwa ACF goyon bayan da take buƙata domin sauke nauyin da ke kanta.”