Kocin Manchester United Eric Ten Hag ya nuna kwarin gwuiwarsa a kan kungiyarsa, inda ya ce nasara a kan Brentford ya nuna cewar Man Utd na dab da dawowa cikin hayacinta.
Manchester United ta samu nasara a kan Brentford a wasan sati na 8 na gasar Firimiya Inggila ta bana a wani yanayi mai ban mamaki.
Brentford tana gaba da ci 1 kafin Scot Mctominay ya shigo ya jefa kwallaye biyu a cikin mintuna hudu kacal.
Abin da ya sa Man Utd dagowa daga matsayi na 13 zuwa matsayi na 10 a kan teburin Firimiyar.