Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), CON yayi kira ga masu daura aure da su yi gwajin kwayoyi (Drug Test) kamar yanda ake yin sauran gwaje-gwajen lafiya kafin daura aure.
Marwa ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci mai martaba sarkin Mubi, Alh Dr. Abubakar Isa Ahmadu a fadarsa da ke garin Mubi a ranar Asabar 24 ga Fabrairu.
- Mata Na Da Jan Aikin Sanin Muhimmancin Kansu Ta Kowane Fanni – Farida Abubakar
- Rikita-rikitar ‘Yar Tiktok Murja Kunya Da Hukumar Hisba A Kano
Shugaban wanda yake gudanar da ziyarar aiki a jihar Adamawa don ganin yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta a jihar ya bayyana cewa, gwajin kwayoyi na daga cikin matakan da zasu rage yaduwar shaye-shaye a tsakanin matasa wadanda sune rukunin da suka fi ta’amuli da miyagun kwayoyi.
Marwa, wanda shine sarkin Arewan Mubi, ya samu rakiyan manyan mukarrabansa da suka hada da shugaban ma’aikata, Lt Kanal Murtala Aminu, Daraktan yada labaru, Femi Babafemi, kwamanda shiyar B, Idris Bello, da kuma Kwamandan hukumar na jihar Adamawa.
Da yake jawabi yayin tarbar tawagar, Mai Martaba Sarkin Mubi ya jinjinawa Janar Marwa, inda ya siffanta shi da wanda Adamawa ke alfahari da shi. “Muna alfahari da kai, zamu ci gaba da baka dukkan goyon bayan da kake bukata. Muna ganin kokarin ka. Shaye-shaye da kuke kokarin raba matasanmu da shi wanda ba karamin musiba ba ne.” Inji Sarkin.