Wata kungiya mai suna ‘Coalition of Northern Group’ ta bukaci a samar da jami’an tsaro na yankin arewacin Nijeriya tare da sa musu suna ‘Arewa Security Taskforce’, za a samar da su ne da nufin tabbatar da tsaro a fadin jihohin arewa.
Shugaban kungiyar na kasa, Kwamarat Jamilu Aliyu Charanchi shi ya bayar da wannan shawarar lokacin da yake magana da manema labarai bayan kammala taron sirri da gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari da mai ba gwamna shawara ta fannin tsaro, Alhaji Ibrahim Ahmad a gidan gwamnati da ke cikin Jihar Katsina.
- ’Yan Bindiga Sun Saki Mutane 43 Da Suka Sace A Masallaci, Sun Kashe Daya A Zamfara
- An Shirya Tattaunawar Tiangong Tsakanin ‘Yan Sama Jannatin Sin Da Matasan Afirka Cikin Nasara
Kwamaret Charanchi ya ce samar da hukumar tsaron ya za ma wajibi idan aka yi la’akari da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da yaduwa a shiyyar arewacin Nijeriya.
Ya ce shawarar samar da jami’an tsaron wani bangare na shawarwarin da aka ba dawa cikin rahoton binciken matsalar tsaro da hanyar magancewa, wanda aka gabatar wa gwamnan lokacin taron.
Ya yaba da tabbacin da gwamnan Jihar Katsinan ya ba da na cewa a matsayinsa na shugaban kwamitin tsaro na kungiyar gwamnonin arewa zai yi nazari a kan rahoton.
Ya ce yin hakan zai ba da damar daukar mataki na bai-daya wajen magance matsalar a fadin yankin na arewa.