An yi nasarar shirya tattaunawar Tiangong wato cibiyar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin, tsakanin ‘yan sama jannatin dake kumbon Shenzhou-14 da wakilan matasa da yaran kasashen Afirka cikin nasara jiya Talata.
Ban da babban wurin da aka kebe a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka wato AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, an kuma kebe wasu wuraren tattaunawa a kasashen Afirka guda 8 wadanda suka hada da Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.
Jakadan kasar Sin dake Nijar Jiang Feng, ya gabatar da wani jawabi a wurin tattaunawar da aka kebe a kasar, inda ya bayyana cewa, akwai dadadden zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kuma tattaunawar Tiangong da aka shirya, ta kara habaka cudanyar dake tsakanin sassan biyu. Ko shakka babu tattaunawar za ta zaburar da nazarin sararin samaniya na matasa da yara na kasashen Afirka.
A yayin taron, wakilan matasa da yaran kasashen Afirka sun kalli faifan bidiyon tattaunawar da aka gabatar, tare da nuna mamaki matuka da irin fasahohin zamani game da nazarin sararin samaniya na kasar Sin da babban sakamakon da ta samu a bangaren da suka gani. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)