Kungiyar manoma wadanda suka kunshi sarakunan noma na kananan hukumomin da ke cikin masarautar Gaya, sun bayyana cewa suna samun tallafi daga sarkin noman masarautar Gaya.
Sun bayyana hakan ne lokacin da suka ziyarci sarkin noman masarautar Gaya, Alhaji Yakubu Ibrahim Tagahu a ofishinsa a ranar Talata da ta gabata karkashin shugabancin sarkin noma na karamar hukumar Garko, Alhaji Shehu Umaru Garko.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
Ya ce su manoman wannan masarauta da manoman wajen masarautar ta Gaya da ke Kano, suna samun tallafi mai dimbun yawa daga Alhaji Yakubu Ibrahim Tagahu.
Alhaji Shehu ya ce sarkin noman masarautar Gaya shahararan manomi ne da ke noma hekta sama da dubu a shekara, kuma yakan samu daruruwan kayan amfanin gona a duk shekara.
Shi ma Alhaji Lawan Ta’anbo, jami’in tuntuba na hadadiyar kungiyar manoma na karamar hukumar Takai, wanda ya yi magana a madadin ayarin kungiyoyin manoman a ziyarar, ya ce sarkin noman masarautar Gaya na zuwa ko’ina a samu iri mai inganci ya gwada shi a kira manoma ya ba domin su amfana.
Ya ce yana bai wa manona gudumawar injina, kudade da shawarwari da kuma bin hakkin manoma ko nemo musu tallafi a matakin gwamnatin jiha ko ta tarayya da sauran kungiyoyin bunkasa aikin noma na Nijeriya.
A karshe shi ma da yake jawabi wanda ya karbi ayyarin kungiyoyin manoman na masarautar Gaya, sarkin noman Gaya Alhaji Yakubu Ibrahim Tagahu, ya ce ba da tallafi ga al’uma umarni ne na addini kuma wajibi ne ga kowa ya yi haka mutukar yana da dama.
Ya kara da cewa umarnin da mai martaba sarkin masarautar Gaya, Dakta Ali Ibrahim Abdulkadir, ya jadada musu wannan umarni a lokacin nadasu kuma haka yake fada musu duk lokacin da ya kira su fada ko kuma suka ziyarceshi, saboda hakan ne zai kawo ci gaban masarautar Gaya da kuma Jihar Kano da ma Nijeriya gaba daya.