Kwanan nan ne kasar Philippines ta yi biris da babbar adawar da jama’ar kasar suka nuna, har ta kaddamar da atisayen soja na shekara ta 2025 mai suna “kafada da kafada” tare da kasar Amurka.
Duk da cewa ita Philippines ta ce ta kaddamar da atisayen sojan ne ba don wata kasa ba, amma jadawalin atisayen ya shaida cewa, na farko, girmansa da kuma adadin kasashe ’yan kallo duk sun kai yawan da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, al’amarin da ya haifar da zaman dar-dar a wannan shiyya. Na biyu kuwa shi ne, Amurka ta yi amfani da wannan dama har ta yi jigilar sabbin makaman kai hari zuwa cikin Philippines, kuma akwai yiwuwar ta girke makaman a Philippines bayan atisayen sojan, abun da ya kara haifar da hadarin yin fito-na-fito a wannan shiyya. Na uku, ba a tsibirin Luzon dake arewacin Philippines kawai aka gudanar da atisayen sojan ba, har ma an yada shi zuwa tsibiran Batan dake kusa da yankin Taiwan na kasar Sin, al’amarin da ya shaida makasudin gudanar da atisayen sojan a bayyane.
Amurka da Philippines sun hada baki don rura wutar rikici a mashigin tekun Taiwan gami da tekun kudancin kasar Sin, domin suna son yin amfani da juna. A bangaren Philippines, tana ganin idan ta tsani kasar Sin kan batun da ya shafi yakin Taiwan, za ta samu karin goyon-baya daga kasar Amurka kan batun tekun kudancin kasar Sin, amma wannan baki daya kuskure ne, kuma sakarci, sa’annan abu ne mai hadarin gaske. Saboda tun tuni kasar Sin ta bayyana cewa, batun yankin Taiwan, babban batu ne mai matukar muhimmanci na moriyar kasar, kuma manufar kasancewar kasar Sin daya tilo, bakin rijiya ne da ba a wargi da shi.
Ba a kan batun tekun kudancin kasar Sin ne kawai Philippines ta rura wutar rikici ba, har ma tana son taimaka wa Amurka kan batun da ya shafi yankin Taiwan, amma muna iya cewa, munafunci dodo ne tabba ya kan ci mai shi, in ji malam Bahaushe. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp