A wani matakin nuna jinkai da tausayawa da ma baiwa mutanen da suka cancanta dama a karo na biyu hade da murnar shiga sabowar shekarar 2024, gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas, ya sanar da yi wa fursunoni 31 Afwa.
Gwamna Kefas, ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa jama’ar jihar jawabin shiga sabuwar shekara, inda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ba da fifiko kan tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
- Ba Za Mu Lamunci Lalaci Daga Waɗanda Aka Naɗa Muƙamai Ba– Tinubu
- Sabuwar Shekara: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Yi Wa Fursunoni 39 Afuwa A Gombe
“A cikin ruhin sabuntawa da ingantawa, ina mai farin cikin sanar da cewa, na yi amfani da ikon da tsarin mulki ya bani, na yafewa fursunoni 31 da suka cancanta.
“Mun kudiri gudanar da wannan shawarar ne domin nuna sadaukarwarmu ga adalci, jin kai, da kuma bada ikon gyara, da fata na gaba” inji Kefas.
Haka kuma gwamnan ya amince da matsalar tsaron da jihar ke fuskanta, ya jaddada alkawarin kara zage damtse domin samar da yanayin tsaro mai inganci ga al’ummar jihar baki daya.
Ya ce, “samar da tsaro da kare rayukan jama’a, wani nauyi ne da kundin tsarin mulki ya dora mana, nan da ‘yan watanni masu zuwa za mu ribanya kokarinmu, na ganin mun shawo kan matsalar tsaro a Taraba.
“gwamnati za ta ribanya kokarinta don ganin Taraba ta zama mafaka ga kowa, amma tare da jama’a za mu shawo kan wadannan kalubale, mu tabbatar mun baiwa gwamnati hadinkai, domin jiharmu ta samu ci gaba cikin kwanciyar hankali” inji gwamnan.