Bikin bana na ranar kafuwar kasar Sin karo na 76 na daban ne bisa yadda ya zo lokaci guda da bikin tsakiyar kaka, wato biki na biyu mafi girma a kasar Sin. Don haka ya kunshi bangaren kishin kasa da na sake haduwar iyali don yaukaka zumunci da kauna, inda za a kwashi tsawon kwanaki takwas ana more hutu a kasar.
Baya ga bukukuwa, ranar kafuwar kasar Sin ta shekarar 2025 ta zama wani muhimmin lokaci na zamanantarwar kasar da nasarorinta a fagen kasa da kasa musamman a fannin kirkire-kirkire, bunkasa ci gaban bil’adama da kuma diflomasiyya.
- PENGASSAN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ta Fara
- Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi
Taken bikin ranar a bana “Zamanantarwa domin al’umma” ya nuna cewa, ci gaba ba wai kawai a gudanar da gine-gine da kere-kere ba ne, dole ne a yi ta fuskar da zai shafi inganta rayuwa, da kiyaye al’adu, da kuma tunanin makomar gaba.
Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya.
Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli na samun habaka cikin hanzari, inda karfin samar da sabon makamashi ya ninka zuwa fiye da kilowatts biliyan 2. Walwalar al’umma na kara habaka ta fuskar kiwon lafiya da sauran muhimman harkokin rayuwa ciki har da kula da ‘yan fansho da kaso 95%, kuma tattalin arzikin kasar a matsakaicin mizanin shekara-shekara yana bunkasa da akalla 5.5% tare da ba da gudummawar kusan kaso 30% na ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Kazalika, bikin na bana ya zo a shekarar da kasar Sin ta kara azamar sauke nauyin da ke wuyarta a fagen kasa da kasa bisa muhimmiyar shawarar inganta jagorancin duniya (GGI) da shugaba Xi Jinping ya gabatar, gabanin taron cika shekaru 80 da kafuwar MDD. Wannan shawara tare da sauran muhimmai guda uku da shugaba Xi ya gabatar a baya, ba manufofi ba ne kawai, sun kasance sauye-sauye na falsafa da ke kunshe a cikin hikimar “samar da al’ummar duniya mai makoma ta bai-daya”.
Yayin da tsoffin tsare-tsaren da kasashen yammacin duniya suka kakaba wa duniya ke fuskantar hisabi, shawarwarin da kasar Sin ta bayar sun kawo mafita a kan yadda za a dama da bangarori masu yawa maimakon babakeren bangare guda, da yadda ko wace al’umma za ta iya tsara tafarkinta, tare da karfafa mutunta juna da samun ci gaba mai gamewa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp