Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) ta nanata matsayarta na daukan mataki kan jihohin da suka ki aiwatar da sabon mafi karancin albashi na zuwa ranar 31 ga watan Oktoba.
Mataimakin babban sakataren NLC, Chris Onyeka, shi ne ya shaida hakan, ya ce, kungiyar ba za ta lamunce wani karin jan kafa kowa wasu dalilai na neman jan kafa ga aiwatar da sabon tsarin ba.
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
- Super Eagles Ta Hauro Matsayi Na 36 A Jadawalin Duniya Na FIFA
Ya ce sabon tsarin albashi na da matukar muhimmanci, don haka ne NLC ke sa ran jihohi za su amshi lamarin hannu biyu-biyu domin ganin an daina cutar da ma’aikata.
Ya ce, “Mun riga mun bayar da wa’adin kammala komai wanda zai kare ne nan da wannan watan. Zuwa karshen wannan watan, wadanda suka ki fara aiwatar da sabon tsarin albashin za su fuskanci turjiya. Za su gamu da mu sosai.”
A yayin da wa’adin ranar 31 ga Oktoba ya karato na aiwatar da sabon tsarin albashi na Naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi, jihohi da dama daga cikin 36 na fuskantar rashin cimma matsaya kan wannan lokacin.
Yayin da wasu jihohin kuma suka kammala cimma matsaya da kungiyoyin kwadago kan lamarin mafi karancin albashi, yayin da wasu kuma suke kan daukan matakan cimma matsaya.
Sai dai a sabon rahotonin da suke a bayyane, akwai wasu abubuwan da har yanzu ake bukatar sake zama domin cimma matsaya a kansu kan sabon mafi karancin albashin a tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatocin jihohi da na tarayya.
Jihohin Legas da Ribas su ne suka yi bajinta wajen amince da Naira 85,000 a matsayin mafi karancin albashi, yayin da Jihar Delta ta amince da Naira N77,500 inda ita kuma jihar Ogun amince da Naira 77,000.
Sauran jihohin da za su biya sun hada da Ondo – N73,000; Kogi – N72,500; Gombe – N71,500, while Edo, Ebonyi, Jigawa, Kwara, Anambra, Adamawa, da jihar Kano da za ta biya mafi karancin albashi na Naira 70,000.
Jihohin Bauchi, Kurus Ribas, Benue, Akwa Ibom, Oyo, Osun, Abia, Inugu, Filato, da Imo har yanzu suna kan tattaunawa da kungiyar kwadago a jihohinsu kan yadda za su cimma matsayar.