Bayan shafe kwanaki 72 a hannjn masu garkuwa da mutane, wasu da harin jirgin kasan Kaduna ya rutsa da su a karshe dai sun samu ‘yanci.
Rahotanni na cewa sun samu ‘yanci ne ya biyo bayan wata tattaunawar ‘yan bindiga da gwamnatin tarayya kan sakin mutanen da aka sace.
Sanarwar ta sakin nasu ta fito ne daga bakin mai ba, Sheikh Ahmad Gumi, shawara, Malam Tukur Mamu.
Ya kuma tabbatar da cewa jimillar fasinjojin da aka yi garkuwa da su da suka samu ‘yancin nasu a ranar asabar sun kai su 11 da ‘yan ta’addar suka sake su.
Rahoton sakin fasinjojin ya bayyana iron rawar da wasu manyan hafsoshin soji masu ritaya da kuma wani sanannen farfesa suka taimaka wajen sako fasinjojin.