Akalla mutane 12 ne suka rasu a wani hatsarin mota a jihar Neja. Hatsarin wanda ya yi sanadiyyar rasuwar wasu mata hudu da maza takwas a hanyar Lapai zuwa Agaie a jihar Neja.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa, daga cikin mata hudu da suka rasu, uku duka ‘yan gida daya ne.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Sayar Wa ‘Yan Bindiga Da Boko Haram Babura A Neja Da Kaduna
- Sojoji Sun Kai Farmaki, Sun Kashe Ƴan Ta’adda Masu Yawa A Neja
An kuma rawaito rasuwar wasu mutane uku da suka hada da mata biyu da direban motar da wasu da suka samu raunuka a wurare daban-daban, wanda a yanzu haka suna samun kulawa a babban asibitin Lapai.
Hatsarin ya auku ne a sakamakon wani karo da wata motar fasinja mai dauke da mutane 15 ta yi, da wata tirela a kauyen Nami da safiyar Asabar.
Da yake zantawa da manema labarai daga gadon asibiti ta wayar tarho, direban mai suna, Mohammed Baba, ya ce ya taso ne daga dajin Kasuwar Gwari da ke Minna, babban birnin Jihar Neja, kan hanyarsa ta zuwa Katcha, karamar Hukumar Katcha. Ya ce direban tirelar ya yi yunkurin wuce wata mota, inda ya kara da cewa kokarin da ya yi na kula da motar bas din ya ci tura, wanda hakan ya haifar da hatsarin.