Gwamnatin Hamas a Gaza ta bayyana cewa, mutane 195 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a cikin makon nan a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da Falasdinawa ke ciki.
“Wadanda hare-haren ya rutsa da su na farko da na biyun a Jabalia sun zarce 1,000”, in ji wata sanarwa daga ofishin yada labaran gwamnatin Hamas, yayin da take magana kan harin da Isra’ila ta kai a ranakun Talata da Laraba.
- Kotu Ta Dakatar Da Majalisar Dokokin Ribas Daga Tsige Fubara
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
“Mun lissafa wadanda suka rasu 195, 120 sun bace a karkashin baraguzan ginin, sannan 777 sun samu raunuka,” in ji sanarwar.
Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce, mutane 8,796 ne suka rasu, mafi yawancinsu mata da kananan yara tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da wani gagarumin hari ta kasa da ta sama biyo bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.