Mutane 21 ne suka jikkata bayan wata girgizar kasa mai girman maki 5.5 da ta afku a birnin Dezhou da ke lardin Shandong na gabashin kasar Sin da karfe 2:33 na safiyar yau Lahadi.
Ofishin bayar da agajin gaggawa na majalisar gudanarwar kasar Sin da ma’aikatar ba da agajin gaggawa ta kasar Sin, sun kaddamar da shirin ba da agajin gaggawa a mataki na hudu bayan abkuwar girgizar kasar.
Gine-gine saba’in da hudu da ke cikin yankin da girgizar kasar ta faru sun ruguje. Sai dai har yanzu ibtilayin bai shafi harkokin sufuri da sadarwa da samar da wutar lantarki ba, in ji ofishin bayar da agajin gaggawa na lardin, inda ya kara da cewa, babu yoyo a bututun mai da iskar gas a yankin.
An aike da tawagar agajin gaggawa da ceto zuwa lardin Shandong domin jagorantar ayyukan ceto da na agaji bayan girgizar kasar. (Yahaya)