Wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 29, yayin da mutane biyu suka ɓata, an kuma ceto wasu mutane 50 da rai.
Binciken jaridar LEADERSHIP HAUSA ya gano cewa hatsarin ya faru ne a yankin Gausawa na Malale, inda jirgin ruwan yake ɗauke da mutane 90 a lokacin hatsarin.
- Shekaru 80 Na Nasara: Kasar Sin Ta Nuna Gado Mai Kyau Na Yaki Da Zalunci
- Babban Sakataren MDD: Sin Ta Taka Rawar Gani Sosai Wajen Cimma Nasarar Yakin Duniya Na Biyu
An bayyana cewa jirgin ruwan ya tashi ne daga kauyen Tugan Sule da ke gundumar Shagunu, inda mafi yawan fasinjojin mata da yara ne, suna kan hanyarsu zuwa Dugga domin kai gaisuwar ta’aziyya.
Wani da abin ya faru a gabansa ya shaida cewa jirgin ya cika makil da fasinjoji tun daga lokacin da ya bar Tunga Sule, amma matsalar ta fara faruwa a lokacin da suka kai Gausawa, inda jirgin ya kife nan take.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Mun karɓi rahoton hatsarin jirgin ruwa a wani ƙauye mai suna Gausawa da ke yankin Malale a ƙaramar hukumar Borgu,” a cewarsa
Ya ce, “Bisa rahoton jami’inmu na ‘search and rescue’, jirgin ya tashi daga Tugan Sule da ke gundumar Shagunu dauke da mutane 90, ciki har da mata da yara, suna tafiya Dugga domin gaisuwar ta’aziyya.”
Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a sakamakon yawan fasinjoji fiye da ƙima da kuma bugu da katako da ke karkashin ruwa, tare da cewa babu wani daga cikin fasinjojin da ke sanye da rigar kariya (life jacket), duk da umarnin gwamnati game da amfani da ita a jihar.
Arah ya ce an gano gawarwaki 29, an ceto mutane 50 da rai, yayin da mutane biyu saka ɓace ake ci gaba da neman su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp