Mutum uku ne suka lone kurmus a yayin da biyu suka ji mummunar rauni a daren ranan Litinin sakamakon hatsarin mota da ya auku a kan babban hanyar Felele da ke Lokoja zuwa Abuja.
Wadanda lamarin ya faru a kan idanunsu, sun shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare.
- Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Fara Duban Watan Zul-Hijja A Ranar Laraba
- Hare-Haren ‘Yan Bindiga Ya Tilasta Yara 3,000 Daina Zuwa Makaranta A Katsina
Hatsarin ya haddasa cunkoson ababen hawa a kan babban hanyar, sai da jami’an hukumar kiyaye hadura ta kasa suka yi ta kokarin bude hanyar domin bai wa ababen hawa damar wucewa.
Majiyoyin sun yi bayanin cewa wata babbar mota kirar tanka dauke mai da tireloli biyu da ke dauke da sunduki da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja da kuma wasu kananan motoci biyu ne dai lamarin ya shafa.
Ganau sun ce tankar da ke dauke da bakin mai da ke kan hanyarta na zuwa Abuja, ta kauce hanya a tsakanin cocin Living Faith da ke kusa da gidan mai na NNPC da ke Felele a Lokoja.
A sakamakon gazawar birkin motar, inda motar ta afka cikin tirelolin biyu da ke dauke da sundukan, inda ta fadi a kansu kuma nan take ta kama da wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku, a yayin da kuma biyu suka ji mummunar rauni.
An dai turo jami’an tsaro inda lamarin ya faru.