Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa mutane 3,433 ne suka mutu, yayin da 22,162 suka jikkata a cikin haɗurra 6,858 da aka ruwaito a faɗin ƙasar nan cikin watanni tara da suka gabata.
Shugaban hukumar, Shehu Mohammed, ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da gangamin wayar da kai na watannin Ember na 2025 a Abuja, inda ya ce yawancin haɗurran suna faruwa ne sakamakon gajiya ga direbobi, da yin lodin kaya fiye da ƙima, da ɗaukar fasinjoji a manyan motoci masu kaya, da kuma safarar man fetur a jarkoki.
- Jami’an FRSC Sun Mayar Da N6.2m Da Suka Tsinta Bayan Aukuwar Hatsarin Mota A Katsina
- Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho
Ya ce wannan kamfen ɗin na Ember wata al’ada ce da FRSC ke gudanarwa duk shekara domin ƙarfafa wayar da kai game da amfani da hanyoyi cikin tsaro, musamman a lokacin ƙarshen shekara da ake samun cunkoso da yawan tafiye-tafiye.
Mohammed ya ƙara da cewa taken gangamin wannan shekara shi ne — “Ɗaukar Alhakin Tsaronka” — an tsara shi ne domin jan hankalin direbobi su sauya halayensu a kan hanya, duba da cewa kuskurensu ne ke da nasaba da mafi yawan haɗurran da ake samu a faɗin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa a lokacin Operation Zero 2024 (wanda ya gudana daga 15 ga Disamba 2024 zuwa 15 ga Janairu 2025), an samu raguwa a adadin mace-mace, inda aka ruwaito mutane 432 sun mutu da kuma 2,070 suka jikkata cikin haɗurra 533 da aka tabbatar da faruwarsu a lokacin.