Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta bayyana cewa mutane 3,433 sun rasa rayukansu, yayin da 22,162 suka jikkata a hatsarin mota 6,858 da suka auku a faɗin Nijeriya cikin watanni tara da suka gabata.
Babban Kwamandan FRSC, Shehu Mohammed ne, ya bayyana hakan a Abuja yayin ƙaddamar da gangamin yaƙin wayar da kan jama’a na shekarar 2025.
- Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
- Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan
Ya ce yawancin haɗuran sun faru ne sakamakon gajiya yayin tuƙi, ɗaukar kaya da yawa, jigilar mutane a manyan motoci, da kuma safarar mai a cikin kwalaben roba.
Mohammed ya bayyana cewa gangamin na watannin “Ember” na kowace shekara na nufin tunatar da direbobi su kula da lafiyarsu yayin da yawan tafiye-tafiye da zirga-zirga ke ƙaruwar a ƙarshen shekara.
Ya ce taken gangamin na bana: “Ɗaukar Alhakin Tsaro” an zaɓe shi ne domin ƙarfafa wa direbobi gwiwa su guji sakaci da tuƙi tare da ɗaukar matakin kare kansu.
Kwamandan ya ƙara da cewa yayin yaƙin “Operation Zero” na shekarar da ta gabata (Disamban 2024 zuwa Janairun 2025), mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗura 533; adadin ya ragu idan aka kwatanta da na baya.