Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis.
A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin Beijing ta gudanar a yau game da rigakafin ambaliyar ruwa da bayar da agajin gaggawa, an bayyana cewa, bala’in ambaliyar ruwan da ya auku kwanan nan ya shafi mutane sama da 300,000 tare da lalata gidaje 24,000 a birnin Beijing.
Sai dai, yanzu haka birnin na Beijing na kara kokarin farfado da wutar lantarki, da share tituna, da kai muhimman kayayyaki ga mazauna yankin da suka rasa matsugunansu, sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da suka auku sanadin mamakon ruwan sama mai karfi da aka tafka a tsaunukan da ke wajen birnin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp