Aƙalla mutane shida ne suka rasa rayukansu, wasu kuma da suna karɓar kulawa a asibiti bayan ruftawatar wani rami da ake haƙar ma’adinai a kauyen Kissaloi da ke ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato.
Shugaban ƙaramar hukumar Dokta Joshua Riti, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya bayyana alhininsa game da adadin mace-macen da aka samu.
- Da Dumi-Dumi: Wani Abu Ya Fashe A Kasuwa, Mutane Sun Raunata A Jos
- IPMAN Da Matatar Dangote Sun Kulla Yarjejeniya Kan Dakon Mai Kai-Tsaye
Ya ce wajen hakar ma’adinan tana kan iyakar ƙananan hukumomin Bassa da Jos ta Kudu da Jos ta Arewa ne
Yayin da yake jajanta wa iyalan waɗanda Iftila’in ya rutsa da su, Joshua, ya gargaɗi masu hakar ma’adinan da su ci gaba da bin matakan kariya a duk lokacin da suke harkar tonon ma’adanan don kiyaye sake aukuwar makamancin lamarin.
Yawancin waɗanda matasan da ruftawatar ramin haƙar ma’adanan ya rutsa da su ‘yan kasa da shekaru 30 masu jini a jika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp