Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta karyata rahotannin barkewar wata sabuwar cuta a kauyen Gundutse da ke karamar hukumar Kura.
Jami’in yada labarai na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi, a wata tattaunawa ta wayar tarho da LEADERSHIP a jiya, ya ce mutane bakwai ne suka mutu a cikin al’ummar sakamakon tsananin zazzabin cizon sauro da taifod, ba wata sabuwar cuta ba kamar yadda jaridar (national daily) ta rahoto ba.
- Sharhi: Kokarin Fahimtar Yanayin Tattalin Arzikin Sin Ta Bangarorin Ayyuka Guda 3
- Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Shirin Dashen Bishiyoyi Miliyan Uku
Ya bayyana cewa, bayanan da aka samu daga bincike da sa ido na masana (DSNR) a karamar hukumar sun nuna cewa, sananniyar cuta ce – zazzabin cizon sauro da taifod ce da ta bulla a cikin al’ummar a cikin watan Ramadan.
A halin da ake ciki, Abdullahi ya kara da cewa, gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki sun dauki matakan shawo kan lamarin yayin da ake ci gaba da sa ido.