Wani mummunan hatsari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu Bayan da wata babbar mota ɗauke da shanu zuwa kasuwar Gadar-Maiwa, ta kutsa cikin rafi a jihar Bauchi.
Hatsarin wanda ya afku a safiyar ranar Litinin, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar shanu da dama tare da jikkata wasu.
- Gwarzon Wasannin Motsa Jiki Na Shekarar 2024: Bambo Akani
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace Wasu A Sakkwato
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin ya afku ne bayan da motar ta taka wani rami, wanda ya sa tayar motar ta fashe kafin daga bisani ta dungura.
A cewar shaidun, yanayin irin gudun da motar ke yi a lokacin da lamarin ya faru na daga cikin musabbabin afkuwar mummunan hatsarin.
Duk wani kokarin jin ta bakin mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC), reshen jihar Bauchi ya ci tura, inda aka kasa samunsa ta wayar da sakonnin wayarsa, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.