Mazauna garuruwa daban-daban a Jihohin Neja da Kwara, sun tsere daga gidajensu, sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai musu. A Jihar Neja, da yawan mazauna Karamar Hukumar Mariga, sun yi gudun hijira a ranar Litinin sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai musu.
Har ila yau, ‘yan bindigar sun kai farmaki a yankunan da lamarin ya shafa, tun daga karfe 11 na safe har zuwa karfe 5 na yamma, inda suka yi awon gaba da shanun mazauna garin. An kuma samu labarin cewa, ‘yan bindigar sun tafi da wasu yara da ke kamun kifi a kogi, yayin kuma da aka ce; an harbe wani manomi a kusa da kauyen Dusai.
- Al’umma Da Ƴan Bindiga Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Katsina
- Ranar Hausa: Masana Sun Bayyana Bunkasa Da Tasirin Harshen A Duniya
Wakilinmu ya tattaro cewa, a halin yanzu mazauna garin Ragada da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su, sun samu mafaka a Gulbin-Boka da ke Karamar Hukumar Mariga.
Da aka tuntubi Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed mai ritaya, ya tabbatar da faruwar al’amarin, amma ya ce; jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.
Haka zalika, mazauna Ndanaku da ke Karamar Hukumar Patigi a Jihar Kwara, sun kauracewa wurin sakamakon hare-haren ‘yan bindiga. Kazilika, harin na zuwa ne makwanni kadan bayan faruwar makamancin haka a garin Babanla da ke Karamar Hukumar Ifelodun.
Kwamandan ‘yan banga, Gina Gana; wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa; an kai hare-hare guda biyu ne kwanaki uku da suka gabata, wanda ya tayar wa da kowa hankali a garin.
Har wa yau, a makon day a gabata ne Gwamna AbdulRahman AbdulRazak, ya yi taro da wasu masu ruwa da tsaki na Ifelodun, inda ya yi bayani dalla-dalla kan kokarin da suke yi na magance matsalar rashin tsaro. Da yake magana a kan hadin gwiwa da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da sauran dukkanin hukumomin tsaro, gwamnan ya bayyana cewa; ana yin dukkanin abin da ya kamata, domin kawar da duk wata barazana ta tsaro a jihar, ciki har da Ifelodun, Patigi da Edu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp