An tabbatar da mutuwar mutum daya tare da kwantar da wasu fiye da 60 a asibiti sakamakon barkewar cutar kwalara a cikin al’ummomin karamar hukumar Kanam ta jihar Filato.
Shugaban karamar hukumar, Ayuba Musa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata ta bakin mai taimaka masa kan yada labarai, Mazadu Ali, ya ce cutar ta fara ne a garin Ngyang, Kwalmiya, Banak da Bakin Kogi, daga bisani kuma ta bazu zuwa Dengi hedkwatar karamar hukumar Kanam. .
- Babu Wata Kasa Da Za Ta Ce ”Ita Kadai Ta Isa Gayya”
- Dan Nijeriya Lookman Na Kan Gaba Wajen Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika Ta Bana
Ali ya ce, fiye da mutane 60 ne ke kwance a babban asibiti da sauran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da ke Dengi da kuma wasu asibitoci masu zaman kansu a karamar hukumar.
“Dangane da rahoton barkewar cutar, karamar hukumar Kanam ta dauki kwararan matakai don dakile cutar kwalara inda ta rarraba kayan aikin jinya cikin sauri ga mahimman wuraren kiwon lafiya.
“Bugu da kari, karamar hukumar ta biya kudin magani ga duk majinyatan da ke karbar magani, ba tare da la’akari da cewa an kwantar da su a asibitocin gwamnati ko na masu zaman kansu ba.
“An dauki wannan nauyin don tallafawa iyalan wadanda iftila’in ya afkawa don rage musu radadin kashe kudaden kiwon lafiya da ba zato ba tsammani a wannan lokaci mai wahala,” inji shi.