Bisa alkaluman da hukumar lura da shige da fice ta kasar Sin ta fitar, an ce, yayin hutun Bikin Bazara na shekarar nan ta 2024, hukumomin bincike na kwastam na kasar sun tabbatar da cewa, mutane miliyan 13.517 sun shiga ko fita daga kasar a lokacin hutun Bikin Bazara, inda matsakaicin adadinsu ya kai miliyan 1.69 a kowace rana, adadin da ya karu da ninki 2.8, idan aka kwatanta da lokacin hutun Bikin Bazara na shekarar 2023, kuma ya kai kusan kashi 90 cikin dari na makamancin lokacin hutu na Bikin Bazarar shekarar 2019.
A cikin adadin, ranar da aka fi samun yawan zirga-zirgar fasinjoji ita ce ranar 12 ga watan Faburairu, inda adadin mutanen da suka shiga ko fita daga kasar Sin ya kai miliyan 1.857. (Safiyah Ma)