Mutanen garin Bimasa a ƙaramar hukumar Tureta ta Jihar Sakkwato sun kai wa ‘yan bindiga farmaki, tare da kuɓutar da mutanen da aka sace, inda suka kashe sama da 10 daga cikinsu.
Mutanen ƙauyen sun bi ƴan bindigar zuwa daji, inda suka yi musu luguden wuta, suka kashe aƙalla 10 daga cikinsu.
- Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa
- Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno
Haka kuma, sun ceto mutanen da aka sace, sun kuma ƙwato dabbobin da aka sace, tare da kama wani ɗan bindiga guda ɗaya.
Shugabannin al’umma sun yaba wa jarumtakar mutanen, amma sun yi gargaɗin cewar maharan na iya kawo harin ramuwar gayya, inda suka nemi gwamnati ta ƙara tsaro a yankin.
Shugaban ƙaramar hukumar Tureta, Aliyu Tureta, ya tabbatar da lamarin, amma ya ce an kashe ‘yan bindiga guda shida ne kacal tare da ƙwato shanun mutane.
Ƙaramar hukumar Tureta na fama da matsalar tsaro, inda hare-haren ‘yan bindiga ke yawan faruwa, inda suke kashe mutane.
A baya, ɗaruruwan mazauna yankin sun yi zanga-zanga suna neman gwamnati ta kawo musu ɗauki.
Matasa kuma sun yi barazanar ɗaukar makamai domin kare kansu idan gwamnati ta gaza samar da tsaro.